Fassarar Ali Kakaki
Ba
su da ra'ayin siyasa, ba su da bangaranci amma duk da haka suna bayar da
gudummawa ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki ta hanyar samar da ayyukan
da suka dace, shirye-shiryen tallafawa da kuma tallafin karatu.
A
matsayinsu na masu taimakon al’umma, Farfesa Abubakar Adamu Gwarzo da Injiniya
Kale Kawu Agaka, sun nuna cewa bada mukamin siyasa kawai ba, mutum na iya yin
kyakkyawan tasiri ta hanyar samar da ayyukan ci gaba a al’ummarsa da ma kasa
baki daya.
A
lokuta daban-daban a kuma taruka mabambanta, na ci karo da mutanen nan biyu na
ƙarnin X kuma na lura da dimbin kuzari da arzikin da suka yi amfani da shi
wajen tabbatar da ci gaban al'umma.
Gwarzo,
hamshakin dan kasuwa na duniya, Farfesa ne a fannin Harsunan zamani na Turawa (Faransanci),
kuma shi ne wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha ta Nijeriya (MAAUN), ya zuba dimbin
jari sosai a manyan makarantun kasar nan domin tabbatar da samar da ilimi mai
inganci a kasar nan.
Agaka,
Injiniyar lantarki kuma Darakta a hukumar samar da wutar lantarki ta yankunan Karkara
(REA), ya tabbatar tare da kuma kula da samar da ingantattun na’urorin wutar
lantarki a al’ummomi daban-daban a fadin Nijeriya.
Kasa
da shekara guda da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta bayar da lasisin
gudanar da aikin Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN)
a harabarta ta Kano, wato a ranar Litinin 15 ga Fabarairu, 2021, Farfesa Gwarzo
har ya gina hanyoyi masu nagarta a yankin, titin masu tafiya a kafa, tare da koriyar
ciyawa da kuma shimfida kyakkyawan furanni. Ya zuwa watan Maris din wannan
shekara, har ya riga da ya kammala kyawawan gine-gine, kamar gine-ginen Tsangayoyin
karatu, dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, gidajen ma’aikata, wajen cin
abinci, wajen wasanni, da dai sauransu, a cikin birnin Kano.
Duk
da kasancewarsa daya daga cikin mafi kyawun jami'o'i masu zaman kansu a
arewacin Nijeriya a yau, wanda ya kirkiro Jami’ar ya yi kokarin saukaka kudin
karatun daliban da ke karatun digiri a kasa da N1,000,000 (naira miliyan daya)
a kowanne zangon karatu. Darussan da aka amince da su domin fara karatunsu a
cikin Jami'ar suna ƙarƙashin Makarantun Gudanarwa (Schools of Management),
Kwamfuta da Doka (Computing and Law). Sannan kuma akwai Makarantar Kimiyyar
Kiwon Lafiya, wacce É—alibai za su iya karatun Unguwanzoma (Nursing), Kimiyyar gwaje-gwajen
lafiya (Medical Laboratory Science) da kuma lafiyar jiki (Physiotherapy).
Gami
da karawa bisa ga abubuwan da ake da su masu nagarta a Jami’ar, ta hanyar
shirinsa na taimakon jama’a, AAG-Foundation, Farfesa Gwarzo ya ba da gudummawar
motoci da motocin daukar marasa lafiya ga wadansu zababbun manyan makarantun
ilimi a Arewa maso yammacin Nijeriya. Har ila yau, Gidauniyar tana jagorantar kamfen
domin inganta hanyar samun ingantaccen ilimi, ƙarfafa tsarin kiwon lafiya,
zaburar da mata da matasa domin haɓɓaka daidaiton jinsi.
Dan
kasuwar, wanda ke gudanar da wata Jami’a irin tsarin ta Amurka a Jamhuriyar
Nijar, ya yi alkawarin kafa Jami’ar Franco British International University a
Kaduna da kuma Jami’ar Canada a Abuja nan ba da jimawa ba.
A
yayin da ’yan kasuwa da dama suka gwammace su saka hannun jari a kasuwancin
gidaje da sauran sana’o’i masu tarin yawa, abin a yaba ne sosai ganin yadda
Farfesa Gwarzo ke zuba jari mai yawa a fannin ilimi domin magance tabarbarewar
ilimi da kalubalen da muke fuskanta a kasar nan, musamman a Arewacin Nijeriya.
Kazalika,
Injiniya Kawu Agaka, Basaraken Masarautar Ilorin, a madadin Hukumar Raya Wutar
Lantarki ta Karkara (REA) inda yake rike da mukamin Daraktan ayyuka, yana lura
tare da kula da samar da Tiransifomar wutar lantarki masu inganci, fitillun dake
amfani da hasken rana da kuma kananan tasoshin hasken lantarki, a kokarin ingantawa
tare da tabbatar da tsayuwar hanyar samar da wutar lantarki a sassa daban-daban
na kasar nan.
Baya
ga samar da ci gaban ababen more rayuwa ta tsawo da fadin Nijeriya, Kawu Agaka,
wanda a kwanakin baya Sarki Sulu Gambari ya nada shi a matsayin Dan-Iyan Masarautar
Ilorin, yana ba da tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin garin da kuma shirye-shiryen
koyon sana’o’i domin karfafawa matasa hanyoyin dogaro da kai, tare da tallafa
wa Zawarawa da marayu da magunguna kyauta ta hanyar gidauniyar iyalansa.
Don
haka ba abin mamaki ba ne yadda jama’a daga nesa da kusa da ba a taba ganin
irinsa ba suka yi cincirindo a Fadar Sarkin da ke Ilorin a lokacin bikin nadin
sarautar Dan-Iya. A haƙiƙa, da yawa daga cikin waɗanda suka ci gajiyar
taimakonsa da sauran karamcinsa sun taka rawar gani a cikin wannan bikin Sarauta
ta gargajiya ta hanyar ba da gudummawa mai yawa wajen gudanar da taron.
Sarautar
Dan-Iya yawanci ana yi wa Basarake ne mai gaskiya da hangen nesa kuma wanda ke bada
gudummawa ga al'ummarsa. Ana kuma ganin Agaka a matsayin wanda ya dace da
wannan mukami, wanda mahaifinsa, Marigayi Alhaji Ibrahim Kawu Agaka, Basarake ne
kuma hamshakin dan kasuwa, wanda ya kasance mutum na farko da ya fara rike mukamin.
Injiniya
Agaka ya tabbatar da gaskiyar cewa ma’aikatun gwamnati, a matsayin babban hanyar
hidima, ya kamata a yi amfani da shi wajen amfanar jama’a, domin ci gaban
al’umma da ma kasa baki daya, ba don wata boyayyiyar manufa ba ko son rai ba.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara ya tabbatar da haka a lokacin da ya
bayyana sabon Dan Iyan a matsayin abin alfaharin masarautar Ilorin.
AbdulRazaq
ya ce a gaskiya wannan karramawar ta Sarautar gargajiya ta dace sosai da wanda
aka bai wa saboda kyawawan dabi’un wanda aka karrama, da kaunarsa ga al’adun
Ilorin da kuma yadda yake sadaukarwa wajen tallafawa al’umma.
“Zabensa
a matsayinsa wanda za a bai wa wannan babban matsayi na Sarautar al’ada ya
tabbatar da dimbin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’ummarmu, da goyon
bayansa ga al’adunmu, da manufofinsa na bude kofa da kuma goyon baya, musamman
ga matasa. Lallai mu muna alfahari da shi. Ina godiya ga Mai Martaba Sarkin
Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari, da majalisar Masarautar bisa kyakkyawan
zabar mutumin kirki a matsayin Dan Iyan Geri (Ilorin),” in ji Gwamnan.
A
cikin ayyukanmu masu ma'ana da kuma suka, ya kamata mu kuma yi ƙoƙari a
koyaushe mu taya waÉ—anda ke ba da gudummawa ga ci gaban rayuwar al'umma.
Farfesa Adamu Gwarzo da Injiniya Kale Agaka, a cikin É—imbin sauran jama’a, su
ne abin koyi waÉ—anda ya kamata gudunmawarsu ta zaburar da wasu domin
kwaikwayonsu, idan ba don ’yan Adamtaka ba, ta hanyar sadaukar da kai,
sadaukarwa, da jajircewa wajen ganin an samu ingantacciyar al'umma, wacce za ta
habbaka buƙatun ci gaban ɗan adam.
A
yayin da nake ba wanda ya kafa Jami’ar Amurka da ke Kano, Farfesa Gwarzo
shawara da ya tabbatar da daukar kwararrun masana da gogaggun Malamai domin karantar
da darussan ilimi, kazalika zan kuma bukaci Injiniya Agaka ya ci gaba da rike
matsayinsa na siyasa, tare da tabbatar da daidaito da adalci wajen sauke nauyin
da aka dora masa na ayyukansa da kuma ci gaba da ayyukansa na cikin al'umma ba
tare da kyashi ba. Allah yasa dukkanin waÉ—annan mazajen biyu masu kirki su ci
gaba da samun nasara, gamsuwa da kuma kwarin guiwar yin fiye da abin da suke yi
a yanzu, a yayin da suke ci gaba da kawata mafi kyawun abin da É—an adam yakamata
ya bayar.
Shu’aib, kwararren mai kula da
harkokin yada labarai ne ya rubuto daga Abuja. www.YAShuaib.com