Jami’ar Ahmadu Bello Ta Bai Wa Farfesa Abdullahi Danladi Sabon Mukami

MMS HAUSA
0

 


Daga Ammar M. Rajab

Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ta kafa sabuwar kujerar Farfesa a fannin ‘Polymer’ da ‘Textile Engineering’, inda ta nada Farfesa Danladi Abdullahi a matsayin shugaban kujerar.

Wannan bayanin ya fito ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na Ofishin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ya sanyawa hannu kuma ya aikawa manema labarai a ranar Litinin, 28 ga watan Fabrairu, 2022.

Farfesa Danladi, haifaffen Kerau Quarters ne da ke cikin birnin Katsina a jihar Katsina. An haife shi ne a ranar 4 ga watan Nuwamba, 1962, kuma yana koyarwa ne a Sashin Injiniyar Polymer da Textile na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Nadin nasa wanda shugaban Jami’ar ya amince da shi bayan tattaunawar tantancewa da aka yi masa da shi da wasu mutane uku wanda aka gudanar a ranar 8 ga watan Fabarairu, na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 21 ga watan Fabarairu wacce take dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Rabiu Samaila.

Nadin Farfesa Danladi, a cewar wasikar, “na shekaru uku ne a wa’adin farko kuma za a iya karawa zuwa wani karin lokaci wanda bai wuce shekaru biyu ba idan aka yi aiki mai gamsarwa".

A shekarar da ta gabata, daidai da ranar 2 ga Agusta, 2021, Jami'ar da kuma Gidauniyar Paul da Mary Achimugu suka sanya hannu tare da yarjejeniyar fahimtar juna domin kafa kujerar Shugaban Farfesa a fannin Polymer da Injiniyar Textile a jami’ar.

Kujerar tana da mahimmanci wajen habbaka ci gaban ilimi da kuma neman kwararru a fannin injiniyar polymer da Textile ta hanyar koyarwa, bincike da kuma wallafe-wallafe.

Farfesa Danladi ya fara aiki da Jami’ar Ahmadu Bello a ranar 17 ga watan Agusta, 1987 bayan ya kammala karatunsa a jami’ar a shekarar 1986 a bangaren Fasahar Yadi (Bsc. Textile Technology).

Ya samu kyakkyawan sakamako a digirinsa a mataki na biyu (Second class Upper Division), sannan ya lashe lambar yabo ta Afprint ga mafi kwazon dalibi a sashin Kimiyyar da Fasahar yadi (Textile Science and Technology) na Jami’ar Ahmadu Bello, a shekarar 1986.

Ya kammala karatun Sakandarensa a shahararriyar Kwalejin Gwamnati da ke Kaduna da sakamako na daya (Division one) a jarabawar WASC, ya yi digirinsa na biyu (M.Sc). a bangaren (Textile Technology) da digirinsa na uku (PhD) a bangaren (Polymer Science and Fiber Technology) a Jami'ar Ahmadu Bello a shekarar 1991 da 2008.

Shugaban kujerar, wanda aka kara masa girma zuwa matsayin Farfesa a ranar 1 ga watan Oktoba, 2014, yana da adadin wallafe-wallafen ilimi guda 73 a cikin mujallolin da ake bita. 

Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top