Fashewar ta faru ne a lokacin da masu ibada suka taru a masallacin Kucha Risaldar da ke tsohon birnin Peshawar domin yin sallar Juma'a. Inda ya kashe mutum fiye da 45 da raunata fiye da 60 ya zuwa hada rahoton nan.
Wani bam mai karfi ya fashe a cikin wani masallacin 'yan Shi'a da ke birnin Peshawar a arewa maso yammacin Pakistan a ranar Juma'a, inda ya kashe mutum fiye da 45 tare da jikkata wasu da dama, da dama daga cikinsu sun samu mummunan rauni.
Fashewar ta faru ne a lokacin da masu ibada suka taru a masallacin Kucha Risaldar da ke tsohon birnin Peshawar domin yin sallar Juma'a, in ji 'yan sanda.
Motocin daukar marasa lafiya sun bi ta cikin titunan mai cike da mutane dauke da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Lady Reading. Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
An kai hare-hare makamantan wannan a yankin da ke kusa da kan iyaka da kasar Afganistan.
Shayan Haider, ganau ne, yana shirin shiga masallacin, lokacin da fashewar mai karfi ta jefa shi kan titi.
"da na bude idona, sai na kura da gawarwaki a ko'ina," in ji shi.
A sashen bayar da agajin gaggawa na asibitin Lady Reading, an shiga rudani a yayin da likitoci ke fafutukar matsar da wadanda suka samu raunuka zuwa wuraren tiyata.
Firaminista Imran Khan ya yi Allah wadai da tashin bam din.