Gwamnatin Kano Na Son Yin Katsalandan A Shari’ar Shaikh Abduljabbar

MMS HAUSA
0

-A cewar Cibiyar Tallafa wa Gajiyayyu ta AGB

An zargi gwamnatin Jihar Kano ta Abdullahi Umar Ganduje da yunkurin yin katsalandan a shari’ar da ake yi wa Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara a kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke yi wa jagoranci.

A taron manema labarai da ya kira a karshen mako a Kano, Shugaban Kwamitin Tsare-Tsare na Cibiyar Tallafa wa Gajiyayyu ta AGB (A Grateful Band), Injiniya Ibrahim Abdullahi Warure, ya nuna damuwa matuka a kan bayanan da ke fitowa daga bangarori daban-daban a kan kai-komon da gwamnatin Kano da abokan burminta, Malaman Maja ke yi tun daga ranar 03/03/2022 da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya fara kare kansa a kan tuhume-tuhumen da ake yi masa da nufin canza akalar shari’ar zuwa wani abu na daban.

Injiniya Warure ya tabbatar da cewa, sabbin bayanan sirrin da suka samu daga majiyoyi masu tushe, sun fallasa wasu kulle-kullen da ake yi na kawo wa shari’ar cikas, ta hanyar tilasta wa Alkalin da ke shari’ar ya daure Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ko da bai same shi da wani laifi ba.

A zama biyu na baya-bayan nan da aka yi a ranar 3 da 17 ga wannan watan da muke ciki, Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya warware zare da abawa kan wasu daga cikin tuhume-tuhumen da aka yi masa, tare da gabatar da littattafai 27 da ya dogara da su, ta hanyar daukar zarge-zargen da ake masa guda takwa daya bayan daya yana warware su.

Cibiyar ta AGB, ta ce suna nuna damuwarsu ne bayan sun samu labarin irin matsin lambar da Alkalin yake fuskanta, tare da zama kashi takwas, ciki har da wanda Malaman Maja suka yi a garin Fatakwal babban birnin Jihar Rivers a kan yadda za su bullo wa shari’ar.

“Duk da yake maganar da ke gaban shari’a ba a tattauna ta, ana barin a ga me zai faru ne a kotu, amma sun nuna fargabarmu a kan kai-komin da wadanda suke son lallai sai an samu Shaikh Abduljabbar da laifi suke yi wajen ganin an tauye masa hakkokinsa da dokar kasa ta ba shi.

“Tun farko mai bai halatta kowace irin kotu ta saurari abin da mutum ya yi imani da shi a matsayin addini ko a matsayin Ubangijinsa, kamar yadda kuma ba wata kotu da take da hurumin sauraron wata kara da aka shiga da ake tuhumar wani Malami ya yi fassarar bisa fahimtarsa, ko ya koyar, ko ya tsaya a kan abin da ya fahimta sabanin abin da Malamai suke a kai.

“Kamar yadda masana shari’ar suka tabbatar kotunan Shari’a da muke da shi ba su da hurumin sauraron duk wani abu da ya shafi addini irin wannan, ikon su shi ne maganar gado, aure da sauran abubuwan da suka shafi wannan.

“Kamar yadda masana shari’ar suka tabbatar kotunan Shari’a da muke da shi ba su da hurumin sauraron duk wani abu da ya shafi addini irin wannan, ikon su shi ne maganar gado, aure da sauran abubuwan da suka shafi wannan.

“Ba wata kotu a duniya da take da halaccin tattauna abin da ya shafi imani. Wannan maganar ta Shaikh Abduljabbar ba ta kotu ba ce, ta tattaunawa ce a tsakanin Malamai, kuma su Malaman ba wanda yake da ikon ya tankwara wani Malami ya yi fahimtarsa”, in ji shi.

Daliban Shaikh Abduljabbar, wadanda suka zargi gwamnatin Kano da Malaman Maja da zama kanwa uwar gami a kan wadannan kulle-kullen ganin sun yi wa shari’ar kafar ungulu, sun nuna gamsuwarsu a kan yadda shari’ar ke tafiya, wanda Alkali Ibrahim Sarki Yola ya ba shi damar kare kansa, har da gabatar da littattafai 27, bayan kuwa su suna so ne a daure shi ba tare da an ji bahsin daga bangarensa ba.

“Wannan dai ita ce damar da Shaikh Abdujabbar Nasiru Kabara ya rasa a wajen zaman titsiye da aka kira shi da mukabala da aka yi ranar 8 ga Agusta, 2021. Gangami aka yi tsakanin gwamnati da hadakar kungiyiyin Kadiriyya, Tijjaniyya, Izala da Sallafiyya sun shirya suna son daure shi ko ta halin kaka”, in ji Injiniya Ibrahim Abdullahi Warure.

Kazalika sun nuna damuwa a kan abin da daya daga cikin Lauyoyin gwamnati ya fada wa ’yan jarida bayan an fito zaman kotu na ranar 17 ga wannan watan, inda yake cewa duk wadannan littattafan da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke kafa hujja da su a gaban kotu, ba a matsayin komai suke ba a kan wannan shari’ar, domin dokar Jihar Kano ya karya.

Suka ce duk matakan da ake dauka a kan Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara tun daga watan Fabrairu, 2021 da aka rufe masa masallaci da makarantar As’habul Kahfi, sun yi hannun riga da kundin tsarin mulkin kasar nan, amma ana yin amfani da karfin mulki ne kawai ake takawa da murjewa.

Ya ba da misali da kamun da aka yi wa Barista Hashim Husaini Fagge a cikin watan Nuwamba, 2021 da nufin a rufe masa baki saboda irin yadda yake fito da asalin gaskiyar dalilin da ya sa aka kama Shaikh Abduljabbar, tare da nuna rashin dacewar umarnin da Gwamnan Abdullahi Ganduje ya bai wa Malamai a ranar Litinin 19/7/2021 na su yi hudubar sukar Shaikh Abduljabbar a kan mumbarorinsu.

Injiniya Ibrahim Warure, ya yi kira ga kungiyoyin Lauyoyi na kasa da kasa da ta Nijeriya da sauran kungoyoyin farar hula da na masu rajin kare hakkin bil’adama, su sa ido sosai wajen ganin an yi wa Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara adalci a kan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Daga karshe, Injiniya Ibrahim Warure, ya yi fatan wannan shari’ar da ake yi wa Shaikh Abduljabbar za ta bude sabon shafi wajen hanyar dakile duk wani zalunci da rashin adalcin da za a yi wani a kan imaninsa, ko kuma ’yancin fadar albarkacin bakinsa a nan kasar.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top