Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kama hanyar zuwa birnin London don duba lafiyarsa. balaguron da zai dauke shi tsawon makwanni 2.
Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin fadar shugaban Najeriya Femi Adesina ta ce shugaba Buhari zai fara yada zango a Kenya wajen taron Majalisar Dinkin Duniya gabanin wucewa Birtaniya.
Ko a watan Maris din 2021 sai da shugaba Muhammadu Buhari ya harzaya London wajen duba lafiyarsa ko da ya ke an dakatar da makamanciyar ziyarar a watan Yunin shekarar.
Sanarwar fadar shugaban na Najeriya, ta ce tawagar shugaba Muhammadu Buhari za ta bar kasar a yau talata tare da rakiyar ministan waje Geoffrey Onyeama dana muhalli Sharon Ikeazor baya ga Babagana Monguno da kuma Ambasada Ahmed Rufa’I Abubakar sai Abike Dabiri-Erewa.
Buhari zai kasance a taron na Majalisar Dinkin Duniya har zuwa ranar 4 ga watan nan inda zai gana da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.