Jam’iyyar PRP Ta Ce Samba Ne Shugabanta A Kano

MMS HAUSA
0

 

Daga Muhammad Farouk

Jam’iyyar PRP ta tabbatar da matashin nan, Aliyu Samba a matsayin wanda zai jagoranci shugabancin jam’iyyar a jihar Kano. Bayanin hakan na kumshe ne a sanarwar da Hedikwatar jam’iyyar PRP ta kasa ta fitar, wanda shugabanta na kasa, Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ya sanyawa hannu ya kuma fitar a yau Litinin.

Sanarwar wacce aka yi wa take da; ‘Shugaban Jam’iyyar PRP Ya Tabbatar Da Samba A Matsayin Zababben Shugaban Jam’iyyar PRP A Jihar Kano’, ta jaddada cewa ba ta san wani shugaban jam’iyyar a jihar Kano ba da ya wuce Aliyu Samba. Inda sanarwar ta ce; “Wannan na tabbatar da cewa Malam Aliyu Samba shi ne zababben shugaban jam'iyyar PRP a jihar Kano. An zabi Malam Samba da gagarumin rinjaye ne a taron jam’iyyar da aka gudanar a Kano a ranar Asabar 12 ga Fabarairu, 2022”, in ji sanarwar.

Ta ci gaba da cewa; “A iya saninmu babu wani mai suna Injiniya Abba Namatazu a taron majalisar jihar da aka yi a ranar Asabar 12 ga watan Fabrairun 2022, wanda ya samu halartar wakilai daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano, kashi uku daga cikinsu mata ne; da kuma masu sanya ido a zaben daga Hukumomin zartarwa na tarayya.

“Tuni Injiniya Namatazu da shugabansa Malam Falalu Bello aka sauke su daga mukamansu na shugabancin jam’iyyar a matakin jiha da kasa baki daya. Zaben Samba a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar Kano ya sake tabbatar da rashin shugabancin Namatazu da Falalu Bello a jam’iyyar PRP.

“PRP jam'iyya ce mai bin tafarkin dimokuradiyya wacce ba ta amince da zaman dirshan, na kashin kai ko kuma na son rai ba. Da zarar wa’adin shugaba ya kare, sai a maye gurbinsa da halastaccen zabin jama’a.

“Shugabancin tsofaffi a cikin jam'iyyar wadanda ke adawa da nagartattun matasa da mata da ke taka rawar gani a PRP, sun fi dacewa su tsara tare da daidaita al'amuran dimokuradiyya a cikin jam'iyyar: jama'a suna yanke zabin kansu ne bisa doka, tsarin mulkin jam'iyyar, sannan da kuma, fiye da komai, kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya (na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima), ba wai son rai irin na Falalu Bello ko siyasar dan bangansa, Namatazu ba”, suka tabbatar.

Har wala yau sanarwar ta kara da cewa; “Jam’iyyar PRP a bude take ga duk ‘yan Nijeriya, matasa da Dattawa, mace da namiji, ba tare da la’akari da yanki, kabila, addini, ko akida ba. Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne mutunta dokokin kasa da kuma jigon ka’idojin jam’iyya”.

Sun karkare da cewa; “Ina kira ga kafatanin ‘yan Nijeriya masu kishin kasa, masu mutunta ‘yan adamtaka, ‘yan kishin kasa, ‘yan gurguzu, ‘yan kasuwa masu son kawo ci gaba, matasa, da shahararrun kungiyoyi da su shiga jam’iyyar PRP a yau a fafutukar sake gina siyasa a Nijeriya a matsayin sana’ar yi wa al’umma hidima ba son zuciya ba.”

Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top